Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi kanta
A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da babban sakataren Majalisar, jakadan Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya yi watsi da zargin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi kan Iran tare da bayyana shi a matsayi maras tushe, yana mai cewa wadannan zarge-zarge ba wani abu ba ne illa da’awa ce ta neman kare kanta kan laifukan keta hurumin kasar Lebanon da sojojinta suke yi da ya saba kudurin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701{na Shekara ta 2006} da kuma ayyukanta da suka saba kudurin dakatar da bude wuta da Lebanon.
A wata wasika da ya aike wa shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da babban sakataren Majalisar a jiya Juma’a, Amir Sa’id Irawani, ya bayyana zargin haramtacciyar kasar Isra’ila da cewa zargi ne maras asali da tushe kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin maras makama.
Irawani ya jaddada cewa: “Wannan wasiƙar tashi ta zo ne a matsayin martani ga wasiƙar da aka rubuta a ranar 13 ga Janairu, wannan shekara ta 2025, da wakilin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a Majalisar Ɗinkin Duniya ya aika wa “Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya da Shugaban kwamitin sulhun Majalisar, inda a cikin wasiƙar, ya yi zargi maras tushe da makama kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran cewa, tana fataucin makamai zuwa kasar Lebanon, zargin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi fatali da shi tare da bayyana shi a matsayin maras tushe ko madogara.