Kungiyoyin Falasdinawa Sun Yi Tir Da Sanya Sunan Kungiyar Ansarullah Ta Yemen Cikin Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda

Kungiyoyin Falasdinawa sun bayyana cewa: Sanya kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda da Amurka ta yi alama ce ta girman kungiyar da

Kungiyoyin Falasdinawa sun bayyana cewa: Sanya kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda da Amurka ta yi alama ce ta girman kungiyar da alfaharin Gaza

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun jaddada cikakken goyon bayansu ga kasar Yemen da bangaren kungiyar Ansarullah kan duk wani nau’in hari da Amurka da ‘yan sahayoniyya suke kai musu, wanda na baya-bayan nan shi ne shawarar da shugaban Amurka ya yanke na sanya kungiyar Ansarullahi cikin jerin a abin da Amurka ta kira “jerin kungiyoyin ta’addanci a duniya.

Kungiyoyin gwagwarmayar na Falasdinu sun fitar da sanarwa daban-daban suna yin Allah wadai da matakin na Amurka tare da daukarsa a matsayin hari ne kan al’ummar Yemen da Falastinawa, yayin da bata sunan ‘yan gwagwarmaya tana zuwa ne kan masu gwagwarmaya da bakaken manufofin Amurka da ‘yan sahayoniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments