A jiya Juma’a ne Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky ya girmama ilayan shahidai almajiransa da su ka rasa rayukansa a shekarun baya.
A jawabin da ya yi, Sheik Ibrahim El-zakzaky ya yi kira ga ‘ya’yan shahidan da su cigaba da tafiya akan tafarkin iyayensu shahidai na fada da zalunci’ kamar yadda ya ambata.
Sheikh Zakzaky ya kuma kara da cewa, shahidan sun cika alkawari da nauyin da ya rataya a wuyansu, don haka mun yi imani da cewa suna cikin rayuwa mai dadi.”
Baya ga jawabi, jagoran Harkar musulunci a Nigeria din ya kuma bayar da kyautuka ga iyalan shahidan da kuma yi musu addu’oi na musamman.