Amurka Ta Aike Da ‘Yan –Ci-Rani Ba Bisa Ka’ida Ba Zuwa Guantanamo

Jiragen yakin Amurka biyu dauke da ‘yan gudun hijira da su ka shiga kasar ba tare da izini ba, sun sauka Guantanamo. A ranar Juma’a

Jiragen yakin Amurka biyu dauke da ‘yan gudun hijira da su ka shiga kasar ba tare da izini ba, sun sauka Guantanamo.

A ranar Juma’a ne dai jiragen sojan Amurkan biyu su ka dauki yan ci-ranin da aka kora daga kasar zuwa tsibirin Guantanamo mai bakin suna.

Jirgin farko mai dauke da ‘yan ci-ranin 79 da su ka kunshi mata 31 da maza 48 ya fara sauka a Guantanamo, sannan na biyu da yake dauke da wani adadin da ba tantance yawansu ba.

Sai dai babu cikakken bayani akan ko wadanda aka kai Guantanamon sun hada da ‘yan hijira 538 masu hatsari da aka kama, ko kuma wadanda fadar “White House” ta sanar za a kore su ne daga kasar.

Tun a lokacin da Shugaban kasar Amurka Donald Trump yake yakin neman zabe ne dai ya yi alkawalin cewa korar ‘yan hijira yana cikin abu na farko da zai fara aiwatarwa da zarar an rantsar da shi.

A jiya Juma’a dai sahfin X na fadar mulkin Amurka ( White House) ya wallafa hotunan wasu mutane da aka daure da sarkoki a kafa da hannu ana shigar da su cikin jirgin sama na soja.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadawa ‘yan jarida cewa; Manufar wannan jigilar ta jirgin sama, ita ce korar masu laifi da su ka fi zama hatsari.

Tsibirin Guantanamo ya yi kaurin suna a lokacin gwmanatin George Bush karami saboda yadda aka azabtar da fursunonin da aka kamo daga Afghanistan da Iraki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments