Sha’anin cinikayya daga waje na Iran ya samu tagomashi a a shekarar 2024 idan aka kwatanta da shekarar data gabatace ta.
Cinikin waje na Iran ya kai dala biliyan 126 a cikin watanni 10 na shekarar data gabata..
A cewar hukumar kwastam ta Iran, cinikin kayayakin da ba na man fetur ba na Iran ya kai dalar Amurka biliyan 47.8 wanda ya karu da kashi 17% idan aka kwatanta da na waccen shekarar data gabata.
Mohammad Rezvanifar, mataimakin ministan tattalin arziki da kuma shugaban kwastan na Iran ya ce a cikin watanni 10 na shekarar, ban da fitar da danyen mai, kayayakin fasaha da injiniyanci da lantarki, cinikayya a waje na kasar ya samu rarar fiye da dala biliyan 17, Inda aka fitar da ton miliyan 113 na kayayyaki.
A cikin watanni 10 na shekarar, an fitar da man fetur da darajarsa ta kai dalar Amurka biliyan 29.9, da kayan aikin injiniyanci na dala miliyan 780, da kuma dala miliyan 300 na wutar lantarki.
A cikin wannan lokaci, an fitar da kayayyaki na dala biliyan 11 da miliyan 500 zuwa kasar Sin, da dala biliyan 7 da miliyan 700 zuwa Iraki, dala biliyan 5 da miliyan 200 zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, da dala biliyan 3 da miliyan 500 ga Turkiyya da biliyan daya da kuma Dala miliyan 800 zuwa Indiya.