A wani na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma, kungiyar Hamas ta saki wasu ‘yan Isra’ila hudu a wannan Asabar yayin da ake dakon gwamnatin Tel-Aviv ta saki Falasdinawa 200 a na ta bangare.
Kungiyar Hamas ta bayyana sunayen wasu mata hudu sojojin Isra’ila da ta saki yau Asabar, kuma tuni ta mika su ga kungiyar agaji ta kasa da kasa.
Abu Obeida, kakakin reshen soji na kungiyar, al-Qassam Brigades, ya sanar da sunayen sojojin Isra’ila mata guda hudu, Karina Araiv, Daniella Gilboa, Naama Levy, da Liri Elbaz, wadanda ake shirin sakin.
Gwamnatin kasar ta amince da sakin fursunonin Falasdinawa 50 ga kowace maccen sojin Isra’ila.
Wannan dai shi ne karo na biyu da ake musayar fursunoni bayan da aka sanar da cimma yarjejenitar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, wacce ta fara aiki a ranar Lahadin da ta gabata.
Kungiyar Hamas ta ce za a sako wani fitaccen kwamandan Falasdinawa a bangare na musayar fursunonin ta biyu da Isra’ila bayan tsagaita bude wuta a makon jiya.
Kakakin ya kara da cewa, Zakariyya Zubaidi, tsohon kwamandan kungiyar gwagwarmayar shahidan al-Aqsa a birnin Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan na daga cikinsu.