Kasar Rasha ta sanar da sharadin komawa ga zaman tattaunawa da Amurka
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya jaddada cewa: Farfado da kyakkyawar alaka tsakanin kasashen Rasha da Amurka ya dogara ne kan yadda Amurka ta kare masalaha da muradun Rasha.
Lavrov ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai cewa: “Idan bangaren Amurka ya kare muradu da masalahar kasar Rasha, to, tabbas tattaunawar da za a yi tsakanin kasashen biyu za ta farfado sannu a hankali, amma idan hakan bai faru ba, to al’amura za su ci gaba da kasancewa kamar yadda suke ba tare da canji ba.”
Lavrov ya yi nuni da cewa: Duk da cewa dangantaka za ta iya gyaruwa idan aka kare muradun Rasha, sai dai ba zai yiwu a yi tsammanin wani gagarumin sauyi mai kyau a dangantakar kasashen biyu ba a karkashin gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amurka.