Gambia : Yahya Jammeh Ya Bayyana Aniyarsa Ta Komawa Gida

Tsohon shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh ya bayyana aniyarsa ta komawa kasar. A wani sakon murya da ya aike wa magoya bayansa, Jammeh da ya

Tsohon shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh ya bayyana aniyarsa ta komawa kasar.

A wani sakon murya da ya aike wa magoya bayansa, Jammeh da ya mulki Gambia na tsawon shekaru 23 ya ce yana so ya koma kasarsa da kuma jan ragamar shugabancin jam’iyyarsa ta APRC.

“In shaa Allahu zan dawo”.

‘’Kuna tsammanin ina tsoron zuwa kotu? Da yardar Allah Ta’ala zan dawo ko sun so ko ba su so. »

An dai tilasta ma Yahyah Jammeh barin mulki bayan shan kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Disambar 2016 da Adama Barrow shugaban kasa na yanzu ya lashe, kuma tun lokacin ya ke gudun hijira a Equatorial Guinea.

Kafin hakan dai a baya kungiyar ECOWAS, ta yanke shawarar kafa wata kotu ta musamman ga Gambia da za ta hukunta laifuffukan da aka aikata a cikin shekaru 23 da Yahyah Jammeh ya yi yana mulki.

Sai dai wannan ba shi ne karon farko da tsohon shugaban kasar Gambiya ya sanar da cewa zai komawa kasar ba, inda har yanzu yake da tasiri a harkokin siyasa na kasar.

A shekarar 2022, gwamnatin Gambia ta amince da shawarwarin da kwamitin da ya yi nazari kan ta’asar da aka yi a mulkinta, inda kuma kwamitin ya kuma amince da gurfanar da mutane 70 a gaban kuliya a sahun gaba Yahya Jammeh.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments