Gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta sanar da dakatar da fitar da wani tallafi na kudade ga kasashen waje, in ban da na kawarta Isra’ila da kuma kasar Masar.
A cikin wata sanarwa da sabon sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar ya umurci manyan jami’ai da su “tabbatar da cewa, sun bi umurnin”.
matakin wanda na wucin gadi ne zai kasance na tsawon akalla watanni uku.
Kuma ana ran a cikin kwanaki 85, sakataren harkokin wajen Amurka zai yanke shawarar ci gaban matakin ko gyara, ko dakatar da shi.
tuni kungiyoyin agaji suka nuna kakkausar suka ga umarnin, suna bayyana fargabar cewa hakan na iya haifar da rashin zaman lafiya da asarar rayuka a duniya.
“Ta hanyar dakatar da taimakon ci gaban kasashen waje, gwamnatin Trump na barazana ga rayuwa da makomar al’ummomin da ke cikin rikici, da yin watsi da tsarin da Amurka ta dade tana yi na taimakon kasashen waje bisa la’akari da siyasa,” inji Shugaban kungiyar agaji ta Oxfam ta Amurka, a cikin wata sanarwa.
Wani tsohon jami’in Hukumar Raya Ci Gaban Amurka (USAID), Jeremy Konyndyk, kwatanta matakin ya yi da’’ wauta’’.
Babu wata alama da ke nuna ko matakin ya shafi Ukraine, wacce kusan ta dogara da taimakon makamai na Amurka a yakin da take yi da Rasha tun shekarar 2022.
Amurka ta kashe sama da dala biliyan 60 wajen taimakon kasashen waje a shekarar 2023, fiye da kowace kasa.