Rundunar sojan kasar Lebanon ta sanar da cewa sojojin abokan gaba Isra’ila jan jiki wajen janyewa daga kudancin Lebanon da hakan yake hana su sojojin Lebanon din shiga yankunan yankin.
Sanarwar sojojin Lebanon din da su ka fitar a yau Asabar, ta amabci cewa; A daidai lokacin da kwakani 60 suke cika daga tsagaita wutar yaki a tsakanin Lebanon da abokan gaba Isra’ila, muna yin kira ga mazauna yankin da su dan dakata kar su koma gidajensu dake kan iyaka, saboda har yanzu da akwai nakiyoyi da wasu abubuwa da ake da shakku akan nau’insu, wadanda abokan gaba Isra’ila su ka bari.
Har ila yau sanarwar ta ce, a halin yanzu banagrorin injiniyinmu suna ci gaba da aiki domin bude hanyoyi da kuma tsince albarusai da ba su fashewa, kuma muna bin diddigin abinda yake faruwa ido a bude.
Haka nan kuma sojojin na Lebanon sun zargi sojojin abokan gaba, na HKI da keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ta hanyar rusa gidaje da kona garuruwa.
Tun a kwanaki kadan da su ka gabata ne dai jojojin HKI su ka bayyana aniyarsu ta ci gaba da zama a kasar Lebanon bayan cikar wa’adin kwankai 60 daga tsagaita wutar yaki.
A gefe daya, kungiyar Hizbullah ta yi gargadi akan ci gaba da zaman sojojinIsra’ila a kudancin Lebanon, bayan cikar kwanaki 60, tare da yin kira ga mahukuntan Lebanon da su yi matsin lamba ga kwamitin bangarorin da su ka sanya ido a tsagaita wutar yakin.