Search
Close this search box.

Karin Bayani Kan ‘Yan Takara 6 A Zaben Shugaban Kasar Iran Na 2024

Majalisar shurra ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar a ranar Lahadi 9 ga watan Yunin 2024, sunayen ‘yan takarar da aka amince da su

Majalisar shurra ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar a ranar Lahadi 9 ga watan Yunin 2024, sunayen ‘yan takarar da aka amince da su a zaben shugaban kasa karo na 14.

Jerin sunayen ‘yan takarar da aka amince da su ya kunshi mutane 6 da suka hada da, Mostafa Poormohammadi, Saeed Jalili, Mohammad Bagher Ghalibaf, Alireza Zakani, Amir Hossein Qazizadeh Hashemi da Massoud Pezeshkian.

A cikin wannan bayyanin, za mu yi dubi ne a takaice kan tarihin wadannan ‘yan takara.

  • Massoud Pezeshkian; Ministan Lafiya a cikin majalisar ministocin ta 8 kuma likitan tiyatar zuciya.

An haifi Massoud Pezeshkian a ranar 29 ga Satumba, 1954 a Mahabad, lardin yammacin Azarbaijan, arewa maso yammacin Iran.

Bayan kammala karatunsa na sakandare a shekarar 1973, an aika Massoud Pezeshkian zuwa birnin Zabol da ke Sistan da lardin Baluchistan da ke kudu maso gabashin kasar Iran, don gudanar da aikin soja, inda a nan ne ya fara sha’awar aikin likitanci.

Don haka Massoud Pezeshkian ya sami digiri na biyu a fannin kimiyyar gwaji a shekarar 1975 kuma ya samu karbuwa a fannin likitanci a jami’ar kimiyyar likitanci da ke Tabriz, babban birnin lardin Gabashin Azarbaijan, a arewa maso yammacin kasar Iran, a shekarar 1976.

Massoud Pezeshkian ya rike mukamin ministan lafiya a gwamnatin Mohammad Khatami ta biyu, tsohon shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuma wakilin Tabriz a majalisar shawarar Musulunci (Majles) na Iran wa’adi 5 a jere.

Ya taba zama mataimakin shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran na farko.

Massoud Pezeshkian shi ma ya yi rajistar shiga zagaye na 13 na zaben shugaban kasar Iran, sai dai ba’a amince da takarar shi ba.

  • Mostafa Poormohammadi; Shugaban Cibiyar tattara bayannan Juyin Juya Halin Musulunci / Masanin shari’a  da dokoki a Shari’ar Musulunci  

An haifi Mostafa Poormohammadi a ranar 9 ga Maris, 1960 a birnin Qom, mai tazarar kilomita 150 kudu da Tehran, babban birnin kasar Iran.

Mostafa Poormohammadi ya wuce matakin farko da mafi girma na ilimin shari’a, ka’idojin shari’a da falsafa a Qum da matakin bayan shari’ar Musulinci a Mashhad, Qom da Tehran.

Mostafa Poormohammadi ya fara aikinsa ne a shekara ta 1979 a matsayin mai gabatar da kara na juyin juya halin Musulunci, kuma har zuwa shekarar 1986 ya kasance mai gabatar da kara na lardunan Khuzestan da Hormozgan da Kermanshah da kuma Khorasan na Iran.

Mostafa Poormohammadi ya zama mataimakin ministan leken asiri daga 1997 zuwa 1999.

Mostafa Poormohammadi ya taba rike mukamin ministan harkokin cikin gida a gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta 9 daga shekara ta 2005 zuwa 2008 sannan kuma ya taba rike mukamin shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta kasar daga shekarar 2008 zuwa 2013.

Mostafa Poormohammadi ya rike mukamin ministan shari’a a gwamnati ta 11 ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran (2013-2017).

A halin yanzu, shi ne babban sakataren kungiyar malamai na gwagwarmaya kuma shugaban cibiyar tattara bayanai na juyin juya halin Musulunci.

  • Saeed Jalili : Memba na Majalisar Manufofin Harkokin Waje / Dakta a kimiyyar siyasa

An haifi Saeed Jalili a ranar 6 ga Satumba, 1965 a birnin Mashhad mai tsarki, babban birnin lardin Khorasan-e Razavi, a arewa maso gabashin kasar Iran.

A cikin shekaru takwas na yakin Iraki da Iran, Saeed Jalili ya sha shiga fagen fama a matsayin dalibin sakandare da jami’a.

A watan Janairun 1986, Saeed Jalili shi ne ke kula da bataliya ta 21 ta Imam Reza a yankin Khorasan, ya ji rauni a lokacin aikin Karbala 5, inda ya rasa kafarsa ta dama a asibitin kayen  Shalamche a lardin Khuzestan a kudu maso yamma Iran, saboda rashin kayan aiki. Sai dai kuma Saeed Jalili ya ci gaba da gudanar da ayyukansa a bangaren kayan aiki.

Saeed Jalili ya fara aiki a hukumance a mukamin siyasa a shekarar 1989 a matsayin shugaban ofishin sa ido na ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Sannan ya ci gaba da aikinsa a matsayin mataimakin farko na sashen Amurka a ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Daga shekarar 2007 zuwa tsakiyar shekarar 2013, Saeed Jalili ya rike mukamin sakataren kwamitin koli na tsaron kasar kuma shugaban tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke tattaunawa da kasashen yammacin Turai akan shirin nukiliyar kasar.

A shekarar 2013, ya shiga zaben shugaban kasa karo na 11 kuma ya samu kuri’u sama da miliyan 4 inda ya zo na uku.

Tun daga wannan lokacin ya kasance mamba a majalisar fayyace Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Saeed Jalili ya goyi bayan shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi wanda ya yi shahada a shekarar 2017 ta hanyar jawabai.

Saeed Jalili ya yi rajistar tsayawa takarar shugaban kasa a shekara ta 2021, amma ya yi murabus kwanaki biyu gabanin zaben a gaban shahid Ebrahim Raïssi.

  • Alireza Zakani : Magajin birnin Tehran mai Digiri na Uku a likitancin nukiliya

An haifi Alireza Zakani a ranar 3 ga Maris, 1966.

Alireza Zakani ya sami gurbin aikin likitanci a shekarar 1989 a jami’ar Tehran ta ilimin likitanci kuma a shekarar 1998 ya sami digirin digirgir. Ya ci gaba da karatunsa a fannin likitancin nukiliya kuma ya sami digiri na uku a shekara ta 2004.

Alireza Zakani mamba ne a majalisar kimiyya ta jami’ar Tehran ta ilimin likitanci kuma memba ne a cibiyoyin likitancin nukiliya na Imam Khumaini da asibitocin Shari’a. Ya kasance memban kwamitin kungiyar likitocin nukiliya ta Iran.

Alireza Zakani shi ne wakilin Tehran a majalisar shawarar Musulunci ta Iran (Majles) ta 7 da 8 da ta 9 sannan kuma shi ne wakilin Qum a majalisa ta 11.

Alireza Zakani ya kasance shugaban cibiyar bincike ta majalisa, dan majalisar tsakiya ta daliban jami’ar ilimin likitanci da ke birnin Tehran, shugaban sojojin sa kai (Basij) na daliban jami’ar Tehran da jami’ar kimiyya ta Tehran. kuma mamba a majalisar koli ta kungiyar agaji ta Red Crescent.

Alireza Zakani ya kasance magajin garin Tehran tun shekarar 2021 kuma an nada shi mataimakin shugaban kasa a shekarar 2023.

  • Sayyid Amir Hossein Qazizadeh Hashemi; mataimakin shugaban kasa kuma shugaban gidauniyar shahidai da Tsaffin sojoji / kwararan Likitan tiyantan kunne, hanci da makogoro.

An haifi Seyyed Amir Hossein Qazizadeh Hashemi a ranar 14 ga Afrilu, 1971 a birnin Fariman na lardin Khorasan-e Razavi.

Shi ne mataimakin shugaban kasa na farko kuma wakilin Mashhad a majalisar shawarar Musulunci ta Iran karo na 11.

Sayyid Amir Hossein Qazizadeh Hashemi shi ne wakilin Mashhad a wa’adi na 8 da 9 da na 10 a majlsair dokoki. A wa’adi na 9 da na 10, ya kuma kasance memba a majalisar shawarar Musulunci ta Iran.

Seyyed Amir Hossein Qazizadeh Hashemi likita ne, likitan fida kuma kwararre a fannin ilimin tiyatar kunne hanci da makogoro.

Ya kasance shugaban jami’ar ilimin likitanci da ke lardin Semnan a arewacin Iran na wani lokaci.

Seyyed Amir Hossein Qazizadeh Hashemi memba ne na majalisar tsakiya ta Paydari Front kuma a cikin 2013-2014, mai magana da yawun wannan majalisa.

An nada Sayyid Amir Hossein Qazizadeh Hashemi mataimakin shugaban kasa kuma shugaban hukumar shahidai da kuma harkokin tsoffin sojoji a zamanin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta 13.

Seyyed Amir Hossein Qazizadeh Hashemi ya kasance dan takara a zagaye na 13 na zaben shugaban kasar Iran kuma ya samu matsayi na 4.

  • Mohammad Bagher Qalibaf; Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci (Majles) na Iran/Digiri na uku a fagen Siyasa

An haifi Mohammad Bagher Ghalibaf a ranar 23 ga Agusta, 1961 a Torqabeh, kusa da Mashhad.

Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a shekara ta 1979, da kawar da ayyukan ‘yan adawa da masu adawa da juyin juya halin Musulunci, an kafa rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) bisa umarnin Imam Khumaini, wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran (Rahamar Allah ta tabbata a gare shi).

Don haka Mohammad Bagher Ghalibaf ya shiga IRGC yana dan shekara 18 kuma aka zabe shi a matsayin kwamandan Bataliya ta Imam Reza a shekarar 1982, kuma Bayan shekara daya aka nada shi kwamandan runduna ta 5 Nasr ta Khhorasan.

Mohammad Bagher Ghalibaf ya kasance a gaba tare da manyan shahidai irin su Mahdi Bakeri, Mohammad Ebrahim Hemmat, Hossein Kharrazi, Ahmad Kazemi da Ali Sayyad Shirzai. Shi ma dan’uwan Mohammad Bagher Ghalibaf, Hassan Ghalibaf, ya yi shahada a lokacin Operation Karbala 4.

A cikin 1994, an nada Mohammad Bagher Ghalibaf shugaban hedkwatar gine-ginen Khatam Al-Anbiya.

Ayyuka kamar layin dogo na Mashhad-Sarakhs mai tsawon kilomita 165 wanda ya hada Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Afghanistan, Jamhuriyar Azarbaijan, Kyrgyzstan, Kazakhstan, Tajikistan, Turkmenistan, Uzbekistan, Pakistan da Turkiyya, samar da iskar gas zuwa larduna 5, gina ginin.

Babban tsarin tekun Fasha da babban Dam Karkheh su ne nasarorin da Mohammad Bagher Ghalibaf ya samu a lokacin gudanar da aikinsa a waccen lokacin.

A shekara ta 1997 ne Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada Mohammad Bagher Ghalibaf a matsayin kwamandan rundunar sojojin saman IRGC.

A cikin 2001, Mohammad Bagher Ghalibaf ya kare karatunsa na digiri na uku kuma an yarda da shi a matsayin memba na majalisar kimiyya ta fannin siyasa a Jami’ar Tehran kuma mataimakin farfesa a Jami’ar Tarbiat Modarres.

A shekara ta 2000 ne aka nada Mohammad Bagher Ghalibaf a matsayin kwamandan tabbatar da doka da oda a Iran bisa umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

A wannan lokacin, aka kaddamar da tsarin 110 na yaki da laifuka ta hanyar waya, kuma yana aiki tun daga lokacin. Ya fadada ayyukan ‘yan sanda tare da samar musu da na’urori da kayan aiki na zamani.

Mohammad Bagher Ghalibaf ya zama magajin garin Tehran a shekara ta 2005 kuma ya rike mukamin na tsawon shekaru 12.

A zaben ‘yan majalisar dokokin kasar Iran na shekarar 2019, Mohammad Bagher Ghalibaf ya lashe zaben farko a mazabar Tehran da kuri’u sama da miliyan daya.

Mohammad Bagher Ghalibaf ya tsaya takarar shugaban kasa sau uku, wato a 2005, 2013 da 2017.

A shekarar 2005, ya zo na 4 da kuri’u kusan miliyan 5. Amma, a shekarar 2013, Mohammad Bagher Ghalibaf ya samu kuri’u miliyan 6 a matsayin dan takara na biyu. A cikin 2017, ya janye daga takarar tare da goyon bayan shahid Mirigayi Ebrahim Raïssi.

Tushen bayyanin : Tashar Al-Alam TV

Hotuna : Rumbun ajiya na Iran

An fasara daga shafin parstoday.ir/fr

Tarjama : H. Barka

https://parstoday.ir/fr/news/iran-i125298-obtenez_plus_d’informations_sur_les_6_candidats_de_l’%C3%A9lection_pr%C3%A9sidentielle_en_iran_de_2024

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
2 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments
Shafiu Kabiru
29 days ago

Da kyau Sannunka Da Aiki Malam Hassan . Aikin Ka Nayin Kyau Sosai. Gaisuwa Gareku Ma’aikatan Hausa Radiyo.