Gwamnatin Kasar Kamaru ta yi tir da yadda aka yi amfani da tutar kasarta a wani jirgin ruwan dakon mai na kasar Rasha da ke zirga-zirga ba bisa ka’ida ba a teku.
Kamaru ta nesanta kanta da Jirgin ruwan mai suna Tagor, bayan da hukumomin Faransa suka tsare shi a gabar tekun Brittany da ke arewa maso yammacin kasar a karshen watan Mayu.
Sojojin ruwan Faransa sun sanar da kama jirgin ne, yayin da yake kokarin kauce wa takunkumin da kasashen yamma suka kakaba na haramta cinikin man fetur da kasar Rasha a yankin.
A cikin sanarwarsa da ya fitar, ministan sufurin kasar Kamaru Jean Ernest Masséna Ngallè Bibehe ya yi Allah wadai da amfani da tutar kasarsa wajen zirga-zirgar da jiragen ruwa a tekunan duniya, alhali basu da wata alka da jirgin ko samun izinin yin haka.
Ko a watan Fabrairu da Mayun wannan shekakarar ta 2026, gwamnatin Kamaru ta fitar da sanarwar gargadi da kuma dakatar da ragistan alakar zirga-zirga sufurin jiragen ruwa da kasashe, sakamakon zargin da ta keyi na cewa wasu kasashe na amfani tutar kasar wajen jigilar kayayyakinta inda aka haramta musu isa, ko haramtattun kayayyaki.