Sojojin Iran Za Su Ci Gaba Da Martani Kan Harin Amurka

Hedikwatar tsaro ta Iran ta sanar cewa ba wani fashi wajen mayar da martani game da hare haren Amurka na baya bayan nan. Wannan sanarwar,

Hedikwatar tsaro ta Iran ta sanar cewa ba wani fashi wajen mayar da martani game da hare haren Amurka na baya bayan nan.

Wannan sanarwar, ta biyo bayan hare-haren da sojojin Amurka suka kai kwanan biyun nan kan wurare da dama a kudancin Iran.

Wannan yana nuna wani shan kashi ga sojojin Amurka a wannan fanni, in ji sanarwar.

Hedikwatar ta Khatam al-Anbiya ta jaddada cewa sojojin za su ci gaba da mayar da martani ga harin da Amurka ta kai.

Rundunar ta kuma sanar da rufe mashigar Hormuz gaba daya ga shige da fice na jiragen ruwa na mai da na kasuwanci, sakamakon hare-haren jiragen saman Amurka a kudancin Iran.

Duk wani yunkuri na wucewa ta wajen gabadaya za a dauke shi a matsayin abin hari,” in ji Rundunar.

Rundunar ta bayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan ci gaba da ayyukan ta’addanci na Amurka da kuma kaddamar da hare-haren sojojin Amurka kan sassa da dama na lardin kudancin Hormozgan.

Hukumar ta yi watsi da ikirarin Amurka na cewa jiragen ruwa za su ci gaba da wucewa ta mashigar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted