An bude gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya ta 2026 da kasashen Amurka, Mexico da Canada ke karbar bakunci.
Kusan ‘yan wasan kwallon kafa 1,250 a tawagogin kwallo 48, ne zasu fafata a wasanni 104.
Saidai gasar ta wannan karo ta zo da korafe-korafe da dama wadanda ke da nasaba da tsadar tikitin kwallon, cin zarafi da kuma hana wasu shiga Amurka sakamakon dokokin kin jin baki na gwamnatin shugaba Donald Trump.
Batun hana alkali wasa dan asalin Somaliya halartar gasar, ya janyo hankalin duniya sosai tare da haifar da toshin Allah tsine.
Haka zalika an hana mambobi 15 daga cikin tawagar Iran shiga Amurka, sannan wasu daga cikin na Iraki musamman mai dokar hoton ta ya fuskanci irin wannan matakin.
Dan wasan Iraki shi ma ya fuskanci tsare shi da akayi na tsawon awa goma yana fuskantar tambayoyi, haka su ma ‘yan wasan Senegal sun fuskanci bincike na kusan sa’a 7.
Za’a bude gasar ta bana da soma fafatawa tsakanin Mexico da Afirka ta Kudu.