Ma’aikatar harkokin wajen kasar Yamen ta yi tofin Allah tsine game da sabbin hare-haren da Amurka ta kai ma kasar Iran, kuma ta bayyana wannan mataki a matsayin babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron duniya baki daya.
A cikin wani bayani da ta fitar a yau Alhamis ma’aikatar ta jaddada cewa harin da Amurka ta kaddamar kan kasar iran zai jefa yankin Yammacin Asiya cikin sabon yaki da yake da makoma mai hatsari ga yankin da ma duniya .
haka zalika ma’aikatar ta bayyana goyon bayanta dari bisa dari ga kasar iran kuma ta jaddada cewa jamhuriyar musulunci tana da hakkin kare kanta daga duk wani hari
A bangaren guda kuma kasar iran ta bayyana harin a matsayin na ladabtarwa kuma martani ga sojojin Amurka masu kashe yara kanan da suka kai hari kan wasu wurare na dakarun kare juyin musulunci da ofisoshin yan sanda da kuma yankunan dake filin hawa da saukar jiragen sama na Bandar Abbas.