A Yau Alhamis ne ake fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ta 2026 mai cike da tarihi a Mexico

A yau ne za a fara gasar lashe kofin duniya karo na 23 wacce ke cike da tarihi, ganin cewa ita ce ta farko da

A yau ne za a fara gasar lashe kofin duniya karo na 23 wacce ke cike da tarihi, ganin cewa ita ce ta farko da kasashe uku wato Amurka da Canada da kuma Mexico suka hadu wajen karbar bakuncin tawagogin kasashe 48 da duniya.

Ita dai wannan gasa ta cin kofin duniya an fara ta ne a shekarar 1930, inda hukumar Kwallon kafa ta duniya FIFA ce ke shiryata duk bayan shekara 4, sai dai a shekarun 1942 da kuma 1946 an samu tsaikon gudanar da gasar sakamakon yakin duniya na biyu.

Ƙasashe 8 ne a tarihi suka taba lashe  gasar, inda Brazil ke da 5, Argentina da ke rike da kofin  4, Jamus da Italiya na da 3-3, sai Faransa da Uruguay da ta fara karbar bakuncin gasar ke da 2-2, yayinda Ingila da Spain kowaccensu ta lashe so dai-dai.

Bayan kammala gasar da kasar Qatar ta karbi bakunci a shekarar 2022, jumullar kasashe 80 ne suka taba fafatawa a cikinta.

Wannan gasa da kasashen Amurka da Canada da kuma Mexico za su karbi bakunci, akwai ƴan wasa 1,248 da za su fafata wadanda suka fito daga kungiyoyin kwallon kafa 449 da ke a kasashe 71.

Za’a yi bukin bude gasar ce a Mexico City, inda Mexico za ta fafata da Afirka ta Kudu a filin wasa na Estadio Azteca.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted