Sakataren Tsaron Biritaniya, John Healey, ya sanar da yin murabus a wani lamari da ake ganin zai kasance koma baya ga gwamnatin firaministan kasar Keir Starmer.
Mista Healey ya bayyana rashin amincewarsa da jagoran jam’iyyar Labour game da matakin zuba jari da ake bukata a aikin soja.
Kun kasa, kuma Ma’aikatar Kudi ta ki amincewa da bukatar tattara abunda ake bukata don kare kasar a wannan lokacin da ake kara samun barazana,” in ji ministan a cikin wasikar murabus dinsa ga Keir Starmer, wadda aka wallafa a shafin X.
Wannan murabus na ba zato ba tsammani wani koma-baya ne ga Firaministan jam’iyyar Labour, wanda matsayinsa na siyasa ya ragu tsawon watanni kuma wanda ke fuskantar barazana daga masu adawa da shi, mako guda kafin babban zaben fidda gwani.
John Healey, wanda wani lokacin ake ambaton sunansa a matsayin wanda zai iya zama abokin hamayya ga Keir Starmer a cikin Jam’iyyar Labour, bai fayyace ko zai shiga takarar jam’iyyar ba.
Gwamnatin Keir Starmer ta yi alƙawarin ƙara yawan kuɗaɗen soja kuma ana sa ran za ta bayyana shirinta na saka hannun jari a fannin tsaro kafin taron NATO a ranakun 7 da 8 ga Yuli.
Taron, wanda zai hada kasashe 32 na kungiyar ta NATO a Ankara, zai samu halartar shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya jima yana sukar kawayen saboda kin shiga yakin da ya kaddamar tare da Isra’ila akan Iran.