Iran: Za ta Kare Kanta Daga Duk Wani Harin Amurka Da Isra’ila Kuma Ba Zata Taba Mika Wuya Ga Matsin Lamba Ba.

Jakadan kasar iran na din din din a majalisar dinkin duniya  Amir saeid iravani yace iran za ta kare kanta daga duk wata barazana  ko

Jakadan kasar iran na din din din a majalisar dinkin duniya  Amir saeid iravani yace iran za ta kare kanta daga duk wata barazana  ko hari da Amurka da HKI za su kawo mata,  adaidai lokacin da Amurka ta fara kaddamar da hare hare akanta.

jakadan ya yi wannan bayanin ne kafin Amurka ta kai hari karo na biyu a kasar iran, bayan da shugaban Amurka Donald trump yayi barazanar kai hare-hare kan kasar iran , bayan da ta kai harin martani kan sansanonin Amurka da kadarorinta dake kasashen Jodan Bahrain da kuma Kuwait

yace iran tana amfani da hakkinta na gado ne na kare kanta kamar yadda yake a kudurin majalisar dinkin duniya mai lamba 51, na mayar da martani kan wuce gona da iri da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Washington da Tel aviv soke yi da aka kulla a watan Aprilu,  da ya kawo karshen yakin da ya sabama doka da suka kaddamar kan iran

daga karshe jakadan na iran a majalisar dinkin duniya yace Tehran ba za ta ci gaba da tattaunawa karkashin barazana ba, kuma ba za ta taba mika wuya kan matsin lamba ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted