Nijar ta fitar da sabuwar dokar ta hukunta masu luwadi, wadda ta tanada yanke hukuncin daurin na shekaru ashirin.
A cewar sabuwar dokar, “duk wanda ya aikata ko ya yi yunkurin aikata wani abu mara kyau ko na rashin da’a ko kuma ya aikata ayyukan luwadi ko madigo za a hukunta shi da daurin shekaru biyar zuwa goma” da kuma tarar har zuwa CFA miliyan 100.
Dokar ta fi tsauri, ga “duk wanda ya yi aure da mutum mai jinsi daya,” wanda hukuncinsa zai iya zama daurin shekaru goma zuwa ashirin.