Dakarun sojojin Ruwa Na Kasar Iran Sun yi Barazanar Daukar Mummunar Mataki Kan Duk Jirgin Da Ya Kusanci Mashigar Hurmuz

Jim kadan bayan sabon harin da kasar Amurka ta kai kan kasar Iran da safiyar yau Alhamis, dakarun sojin ruwa na kasar juyin musulunci sun

Jim kadan bayan sabon harin da kasar Amurka ta kai kan kasar Iran da safiyar yau Alhamis, dakarun sojin ruwa na kasar juyin musulunci sun gargadi duk wani jirgin ruwa da kada ya kusanci mashigar Hurmuz ko kuma ya fuskanci mummunan mataki

Babban kwamanda a babbar cibiyar soji ta Khatamul ambiya  ta sanar da rufe mashigar Hurmuz baki daya kuma ta gargadi tankokin mai da suran jiragen kasuwanci da suke zirga-zirga a tekun fasha da tekun oman da kada su bari jiragensu su kusanci mashigar idan kuma ba haka zasu daukesu a matsayin masu hadin guiwa da makiya

mashigar Hurmuz tana daya daga cikin muhimman wurare a duniya da kashi 1 cikin biyar na jiragen man da ake amfani da shi a duniya suke wucewa ,

yan saoi da suke gabata a safiyar yau ce aka samu labarin fashewar wasu abubuwa a lardin Hurmuz da lardunan kudancin kasar, inda sojojin Amurka suka tabbatar da su ne suka kai harin  a matsayin wata sabuwar sokanar fada da kasar iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted