Ana shirin Jana’izar Shahid Ayatollah Ali Khamenei

Masu shirya bukukuwan tunawa da marigayi Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Seyed Ali Khamenei sun sanar da cewa za a gudanar da bukukuwan bankwana, jana’iza, da binne marigayin bayan kwanaki goma na farko na watan Muharram. Sanarwar ta jaddada cewa ana ci gaba da shirye-shirye masu yawa don tabbatar da cewa an gudanar da […]
Hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 13 a kudancin Lebanon

Bayanai daga Lebanon na cewa hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 13 tare da raunata wasu 31 a wannan Talata a wani sabon saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta, kwana guda bayan da aka dakatar da sabon yaki tsakanin Isra’ila da Iran. Wadanda aka kashe sun hada da wani namiji mai shekaru 16 wanda aka kashe […]
Burkina ta soke duk wata gasar kyau a kasar saboda saba al’adu

Burkina Faso ta yanke shawarar dakatar da duk wani gasar nuna kyau a duk fadin kasar, a wani mataki na ingantawa da kuma kiyaye al’adu da dabi’un al’ummar kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Sadarwa, Al’adu, Fasaha, da Yawon Bude Ido ta kasar ta sanar ta ce an dakatar da duk irin […]
Faransa ta hana Ministan Kudi na Isra’ila sanya kafa kasarta

Faransa ta sanar da haramta wa ministan kudi na Isra’ila Bezalel Smotrich sanya kafa a kasar saboda munannen ayyukan yahudawa masu tsatsauran ra’ayi dake haddasa ayyukan tashin hankali a yammacin Kogin Jordan. Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Noël Barrot ne ya sanar da hakan a shafin X a wani mataki wanda ya ce yana da alaka […]
Iran ta yi tir da daftarin da Amurka ta gabatar a IAEA

Iran ta yi Allah wadai da kakkausar suka da yunkurin Amurka na gabatar da daftarin kuduringaKwamitin Gwamnonin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA). Ofishin jakadancin Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ke Vienna ya fitar da wata sanarwar cewa “abin dariya ne gabatar da daftarin kuduri ga Kwamitin Gwamnonin kan ayyukan nukiliya na […]
Iravani : Ana tattaunawa da Amurka don cimma yarjejeniyar karshe

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa ana ci gaba da tattauna da Amurka da nufin cimma yarjejeniyar karshe. Jakadan na Iran kuma wakilinta na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana cewa: “Ana ci gaba da musayar ra’ayoyi da Amurka da nufin cimma yarjejeniya ta karshe.” Mista Iravani ya kara da cewa, Amurka da […]
Ƙwararru A Bangaren Yancin Addini Na MDD Suna Ziyarar Aiki A Tarayyar Najeriya

Manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya kan ‘yancin addini sun fara wata ziyarar makwanni biyu a Najeriya a ranar Litinin, bayan zargin kasar da muzgunawa mabiya addinin kirista a shekarar da ta gabata. A yayin da Amurka ta zafafa lamarin, wanda take ganin an tauyewa mautane damarmaki na gudanar da hakkokin dake kansu na addini da […]
Hamas Ta ce Kashe Falasdinawa 1000 A Yankin Gaza Yana Nuna Irin Kisan Kiyashin Da HKI Ke Yi

kakakin kungiyar gwagwgarmaya ta Hamas Hazeem Qasim ya bayyana cewa kashe falasdinawa kusan 1000 a yankin gaza tun bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a watan oktoban da ya gabata yana nuna hakikanin irin kisan kare dangi da HKI take ci gaba da yi kan alummar gaza. kakakin yayi kira […]
Iran Ta Bukaci Hukumar Fifa Ta Bada Damar Yin Amfani Da Bakin Kyalle A Wasanta Da Kasar Masar Don juyayin Ashura

hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta bukaci hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a hukumance ta ba da dama yan wasan kwallon iran su sanya bakin kyalle a lokacin karawarsu da kasar masar saboda yayi daidai da zagayowar ranar shahadar imam hussaini As, wasan da aka tsara za’a buga ne a ranar 27 ga […]
Shugaban Majalisar Dokokin Labanon Ya Bukaci Isra’ila Ta Fice Daga Dukkan Yankunan Kasar Da Ta Mamaye

Nabih birri shugaban majalisar dokokin kasar Labanon ya bayyana cewa kasar labanon ba za ta amince da abin da ya gaza dakatar da bude wuta ta sama da kasa da ruwa ba, kuma ba tare da wani sharadi ba, kuma ya jinjinawa matsayin da yan gwagwarmaya suka dauka na tsayin daka wajen kalubalantar hare-haren HKI. […]
Qalibaf: Za mu Ci Gaba Da Yaki Da Kuma Diplomasiya Don Kare Hakkokin Alummar Kasarmu

shugaban majalisar dokokin kasar iran mohammad Baqeer Qalibaf ya bayyana cewa iran tana daukar matakai na ganin an kawo karshen yakin da Amurka da Isar’ila ke yi, ta hanyar ci gaba da yaki da kuma tattaunawar diplomasiya a lokacin guda domin kare hakkokin Alummar kasar Iran A cikin wani bayani na sauti da yayi ga […]
Iran Ta Bada Sanarwan Kawo Karshen Yakin Da Ta Fara Kan HKI A Daren Lahadi

Rundunar Khatamul Anbiya(s) ta kasar Iran ta bada sanarwan kawo karshen yakin kimani kwana guda ha HKI bayan ta ladabtar da ita saboda keta jan layin da ta tsallaka dangane da hare hare a unguwar dhahiya ta birnin Beirut na kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto rundunar tana bayanin cewa, […]
IRGC Ta Ce Ta Maida Martani Kan Kamfanin Sinadaran Manfetur Na HKI A Birnin Haifa

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato IRGC, sun bada sanarwan kai hare hare kan kamfanin sinadaran man fetur na HKI da ke birnin Haifa a hare harenta na baya bayan nan a kan HKI. Tare da gargadin cewa idan ta ci gaba da kaiwa kamfanonin sinadaran man fetur na kasar […]
Iran Ta Tabbatar Da Wani Sabon Tsari A Rikicin Gabas Ta Tsakiya Da HKI

Iran ta kawo karshen yakin sa’o’ii 16 da HKI a ranar Litinin da yamma, tare da samar da wani sabon tsari a rikin gabas ta tsakiya tare da HKI. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, kasashen Amurka da HKI basu tsamman kasar Iran zata aiwatar da gargadin da tayi na kaiwa […]
Iran Ta Musanta Kai Hare Hare Kan Kasar Saudia A Yakin Sa’o’i 16

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakaei ya bayyana cewa sojojin Iran basu kai wani hare kan kasar Saudia a yakin sa’o’ii 16 da ta fafata da HKI ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto bakaei yana fadar haka a jawabi ga kafafen yada labarai da ya saba a ko wace […]
Iran Bata Damu Ta Takunkuman Kungiyar Tarayyar Turai Na Baya Bayan nan A Kanta Ba

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren dokokin kasa da kasa da kuma sharia Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran bata bada wani muhimmanci ga takunkuman tattalin arziki wadanda tarayyar Turai ta bada sanarwan kakabawa wasu daddaikun mutane a da kuma wasu sassan IRGC na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran tasnim […]