Burkina Faso ta yanke shawarar dakatar da duk wani gasar nuna kyau a duk fadin kasar, a wani mataki na ingantawa da kuma kiyaye al’adu da dabi’un al’ummar kasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Sadarwa, Al’adu, Fasaha, da Yawon Bude Ido ta kasar ta sanar ta ce an dakatar da duk irin wannan gasa har sai an amince da sabbin dokoki.
A cewar hukumomin kasar, wannan garambawul wani bangare ne na babban kokari na kiyayewa, tattalin al’adun kasar da zamantakewa, da mutuncin dan adam.
Ma’aikatar ta tabbatar da sha’awarta ta tsaftace da kuma tsara bangaren yayin da take tabbatar da habaka dabi’un al’adun kasar.
Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake kara sukar masu shirya gasar kyau kan mayar da hankali kan irin shigar tufafi da masu nuna gasar kyau.