Qalibaf: Za mu Ci Gaba Da Yaki Da Kuma Diplomasiya Don Kare Hakkokin Alummar Kasarmu

shugaban majalisar dokokin kasar iran mohammad  Baqeer Qalibaf ya bayyana cewa iran tana daukar matakai na ganin an kawo karshen yakin da Amurka da Isar’ila

shugaban majalisar dokokin kasar iran mohammad  Baqeer Qalibaf ya bayyana cewa iran tana daukar matakai na ganin an kawo karshen yakin da Amurka da Isar’ila ke yi, ta hanyar ci gaba da yaki da kuma tattaunawar diplomasiya a lokacin guda domin kare hakkokin Alummar kasar Iran

A cikin wani bayani na sauti da yayi ga alummar kasar qalibaf ya ce iran a shirye take ta ci gaba da ayyukan soji wajen mayar da martani kan duk wani wuce gona da irin Amurka da Isra’ila, idan suka ci  gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a farkon watan Aprilu

wadannan bayanai suna zuwa ne bayan da iran ta kaddamar da hare-hare da makamai masu linzami kan HKi a matsayin martani kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da take yi na kai hare-hare a yankun daban daban a kasar labanon,

Qalifab da yake jagorantar tawagar iran wajen tattaunawa da Amurka ya kara cewa sun yi bakin kokarin wajen ganin an yi amfani da diplomasiya don kawo karshen yakin da ake yi . yace a fili yake cewa bamu amince da Amurka ba duk da tattaunawar da ake yi,  babban burinmu  shi ne a kawo karshen yaki da samar da tabbataccen zaman lafiya, ba wai a kyautata dangantaka da Amurka ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted