IRGC Ta Ce Ta Maida Martani Kan Kamfanin Sinadaran Manfetur Na HKI A Birnin Haifa

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato IRGC, sun bada sanarwan kai hare hare kan kamfanin sinadaran man fetur na HKI

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato IRGC, sun bada sanarwan kai hare hare kan kamfanin sinadaran man fetur na HKI da ke birnin Haifa a hare harenta na baya bayan nan a kan HKI.

Tare da gargadin cewa idan ta ci gaba da kaiwa kamfanonin sinadaran man fetur na kasar to kuwa tana iya fadada maida martani zuwa wasu kasashe a yankin, kuma Amurka ce da laifin duk abinda ya faru idan sun sake maimaita wannan kuskuren.

A wata sanarwa ta musamman wanda rundunar IRGC ta fitar da bayyana cewa, bayan hare haren da Amurka da HKI da kuma kawayensu suka kai kan wani kamfanin samar da sinadaran man fetur na kasar Iran a kudancin kasar, rundunar ta maidamartani a kan kamfanin sinadaran man fetur na Haifa a HKI a ranar Litinin da kuma wasu wurare.

Bayanin ya kara da cewa HKI ta yi babban kuskure da ta kai hare hare kan wuraren fararen hula da kuma kan kamfanonin samar da kayaki ban a yaki ba a hare haren da ta kawo Iran a baya bayan nan.

A safiyar ranar litinin ne wasu kafafen yada labarai a nan kasar Iran suka bada labarin cewa Amurka da HKI sun kai hare hare kan kamfanin Karoun na sinadaran man fetur da ke garin Mahshahr a kudancin kasar hare-haren da suka lalata wani bangare na kamfanin.

Bayan hare haren ne gwamnatin yankin na budaddiyar kasuwa ta bada umurnin fitar da dukkan ma’aikata wadanda aikinsu ba wajibi ba daga kamfanin, amma aka bar wadanda ayyukansu ya zama lazimi don kada a tsaida aiki a kamfanin kwata-kwata.

Labarin ya kara da cewa, babuwanda aka kashe ko aka jiwa raunin a hare-haren Amurka da yahudawan. Kafin haka IRGC ta ce ta cilla makamai a kan sansanin sojojin HKI mafi girma Ramat Devid tare da amfani da makamai masu linzami samfurin Balistic. Daga wannan sansanin jiragen yakin HKI suke kaiwa kasar Lebanon hare hare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted