Iravani : Ana tattaunawa da Amurka don cimma yarjejeniyar karshe

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa ana ci gaba da tattauna da Amurka da nufin cimma yarjejeniyar karshe. Jakadan na Iran kuma wakilinta na

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa ana ci gaba da tattauna da Amurka da nufin cimma yarjejeniyar karshe.

Jakadan na Iran kuma wakilinta na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana cewa: “Ana ci gaba da musayar ra’ayoyi da Amurka da nufin cimma yarjejeniya ta karshe.”

Mista Iravani ya kara da cewa, Amurka da Iran, suna ci gaba da “musayar ra’ayoyi domin cimma matsaya ta karshe ta hanyar Pakistan.

Jakadan na Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce: “Ba mu kammala rubutun ba tukuna, amma muna sa ido kan tsarin.”

Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya kuma jaddada cewa tsagaita wutar dole ya shafi dukkan yankin, ciki har da Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted