Iran Bata Damu Ta Takunkuman Kungiyar Tarayyar Turai Na Baya Bayan nan A Kanta Ba

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren dokokin kasa da kasa da kuma sharia Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran bata bada

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren dokokin kasa da kasa da kuma sharia Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran bata bada wani muhimmanci ga takunkuman tattalin arziki wadanda tarayyar Turai ta bada sanarwan kakabawa wasu daddaikun mutane a da kuma wasu sassan IRGC na kasar Iran  ba.

Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na EU Kaja Kallas ta bada sanarwa a jiya litinin kan cewa kungiyarta ta dorawa wasu daddaikin mutane da kuma wani bangare na dakarun IRGC takunkuman tattalin arziki saboda rawar da suka take wajen rufe mashigar ruwa ta Hurmuz, wacce ta shafi kasashen duniya daga ciki har da kasashen Turai.

Gharibabadi ya ce, wannan sanarwan ta munafurci ne, saboda sun yi watsi da dukkan abubuwan da suka faru kafin Iran ta rufe mashigar ruwam ba. Kuma abunda EU tayi ci gaba ne da adawar da takewa JMI na shekaru aro aro wand aba zai taba sauyawa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted