Iran Ta Bada Sanarwan Kawo Karshen Yakin Da Ta Fara Kan HKI A Daren Lahadi

Rundunar Khatamul Anbiya(s) ta kasar Iran ta bada sanarwan kawo karshen yakin kimani kwana guda ha HKI bayan ta ladabtar da ita saboda keta jan

Rundunar Khatamul Anbiya(s) ta kasar Iran ta bada sanarwan kawo karshen yakin kimani kwana guda ha HKI bayan ta ladabtar da ita saboda keta jan layin da ta tsallaka dangane da hare hare a unguwar dhahiya ta birnin Beirut na kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto rundunar tana bayanin cewa, idan gwamnatin Isra’ila ta sake keta wannan jan layin rundunar tana a nan a madakata. Bayanin Rundunar  ya kara da cewa ‘bayan ayyukan ta’addancin da sojojin HKI masu zubar da jinin mutane a kudanci da kuma unguwar dhahiya na birnin Beirut.

Sojojin JMI masu karfi sun cilla makamai masu lunzami kuma masu karfi kan wasu wurare a kasar Falasdinu da aka mamaye, sun kuma dandanawa azzalumai radadin da yakamata su sha, daga karshen mun kawo karshen hare haren, inji kakakin Khatamul Inbiya(s).

Ta ce wannan wani darasi ne ga gwamnatin yahudawa da kawayensu, don haka rundunar ta bada sanarwan kawo karshen hare hare.

Sai dai ta kara da cewa, tsaida yakin ba nuna gazawa bane, sai dai dama ladabtarwa ga gwamnatin mai kashe yara, mai kuma kishin zubar da jinin mutane.

Ta kara da cewa idan yahudawan sun ki daina hare hare hatta a kudancin kasar Lebanon, zasu gamu da wani sabon farmaki wanda zai wuce wanda ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted