Faransa ta sanar da haramta wa ministan kudi na Isra’ila Bezalel Smotrich sanya kafa a kasar saboda munannen ayyukan yahudawa masu tsatsauran ra’ayi dake haddasa ayyukan tashin hankali a yammacin Kogin Jordan.
Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Noël Barrot ne ya sanar da hakan a shafin X a wani mataki wanda ya ce yana da alaka da “sabbin takunkumi kan wadanda ke da alhakin tsananta muggan laifuka a Yammacin Kogin Jordan”.
Matakin ya kuma shafi wasu “shugabannin kungiyoyin yahudawan ‘yan kama wuri zamna guda hudu shiga Faransa.
Wannan shi ne karo na biyu a gwamnatin Isra’ila da faransa ta doki irin wannan matakin akansa, bayan Ministan tsaron Isra’ila Itamar Ben-Gvir, wanda aka haramta shiga masa Faransa tun ranar 23 ga Mayu, bayan fitar da wani bidiyo da ke nuna ‘yan fafutuka na “Flotilla na Gaza” suna durkusawa da hannuwansu a daure.
Bayan Faransa, kasashen Australiya, Kanada, Norway, da Birtaniya, sun sanar a ranar 10 ga Yuni, 2025, cewa za su haramta wa ministocin Ben Gvir da Smotrich shiga yankunansu, suna zarginsu da “haifar da tashin hankali” ga Falasdinawa, musamman a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
Gwamnatin Birtaniya a wannan Talata ta yi kira ga kamfanonin Birtaniya da su dakatar da duk wani aiki a matsugunan Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, in ji Sakatariyar Harkokin Wajen kasar Yvette Cooper.
Gwamnatin Isra’ila ta yi Allah wadai da wadannan takunkumin tana mai cewa “abin takaici ne.”