Hamas Ta ce Kashe Falasdinawa 1000 A Yankin Gaza Yana Nuna Irin Kisan Kiyashin Da HKI Ke Yi

kakakin kungiyar gwagwgarmaya ta Hamas Hazeem Qasim ya bayyana cewa kashe falasdinawa kusan 1000 a yankin gaza tun bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar

kakakin kungiyar gwagwgarmaya ta Hamas Hazeem Qasim ya bayyana cewa kashe falasdinawa kusan 1000 a yankin gaza tun bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a watan oktoban da ya gabata yana nuna hakikanin irin kisan kare dangi da HKI take ci gaba da yi kan alummar gaza.

kakakin yayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da ta tantance bangaren dake kawo cikas a yarjjejeniyar da aka kulla, kuma ya dauki mataki akansa wajen tillasta masa yayi aiki da nauyin dake wuyansa,  hakazala Qasim yayi kira ga kasashen larabawa da kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC da su dauki mataki mai muhimmanci don dakatar da ci gaba da kiran kare dangin da HKI take ci gaba da  yi wa Falsdinawa

daga karshe kakin na Hamas ya bukaci gwamnatin  falasdinu ta umarci dukkan  jakadunta a fadin duniya su farfado da yunkurin diplomasiya na nuna goyon bayan Alummar Gaza, kuma su muhimmantar da ayyukansu wajen bayyana irin halin kunci da alummar gaza ke ciki da zaluncin da HKI take ci gaba da yi a yankin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted