Iran Ta Tabbatar Da Wani Sabon Tsari A Rikicin Gabas Ta Tsakiya Da HKI

Iran ta kawo karshen yakin sa’o’ii 16 da HKI a ranar Litinin da yamma, tare da samar da wani sabon tsari a rikin gabas ta

Iran ta kawo karshen yakin sa’o’ii 16 da HKI a ranar Litinin da yamma, tare da samar da wani sabon tsari a rikin gabas ta tsakiya tare da HKI.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, kasashen Amurka da HKI basu tsamman kasar Iran zata aiwatar da gargadin da tayi na kaiwa HKI hare hare idan ta kaiwa birnin Beirut hare hare ba.

Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun keta umurnin sojoji da gwamnatin kasar Iran da wasu sa’o’ii sai Iran ta cilla makamai kan HKI ta kuma cika al-kawalin da ta yin a zata yi hakan.

Wannan kuma ya sauya tsarin rikicin gabas ta tsakiya tare da HKI. Inda a halin yanzu sai ta yi lissafi kafin ta kaddamar da wani abu a yankin.

Banda haka a wannan yakin na kimani kwana guda ya kara tabbatar da tsarin kawancen masu gwagwarmaya a yankin inda, Yemen da Iraki da Lebanon da Iran duk sun hade kan yahudawan a lokaci guda,

Dama tun farkon tsaida budewa juna wuta a yakin kwanaki 40 Iran tace sai an tsaida yaki a dukkanin wuraren da ake yaki daga ciki har da kasar Lebanon, amma Amurka da yahudawan suka saba. A halin yanzu wannan yaki na sa’o’ii 16 sun tabbatar da wannan kawancen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted