Nabih birri shugaban majalisar dokokin kasar Labanon ya bayyana cewa kasar labanon ba za ta amince da abin da ya gaza dakatar da bude wuta ta sama da kasa da ruwa ba, kuma ba tare da wani sharadi ba, kuma ya jinjinawa matsayin da yan gwagwarmaya suka dauka na tsayin daka wajen kalubalantar hare-haren HKI.
Birri ya fadi hakan ne a jiya litinin da dare kuma ya ce bayan dakatar da bude wuta ta kowanne bangare ne za’a fara tattaunawa kan yadda sojojin HKI za su fice baki daya daga yankunan kasar labanon, yace ban amince da batun yankunan gwaji ba, na yarda da janyewar sojojin Isra’ila ne da kuma maye gurbinsu da sojojin labanon kafin daga bisani sauran mutane da suka tsere su dawo gadajensu.
A wani bangare kuma kungiyar hizbullah tayi suka mai zafi ga ikirarin karya da shugaban Amurka Donald trump yayi na yi mua’amala kai tsaye da yan adawa a kasar labanon,
babban jami’in hizbulla da kuma mataimakin shugaban kula da bangaren siyasa Mahmud Qamati ya bayyana cewa babu wata tattaunawa ta kai tsaye tsakanin yan adawa da trump ,ya karyata bayanan da Amurka ta fitar, kuma yace wani makirci ne na haifar da matsala a kokarin diplomasiya da ake yi.
bayanan da Nabi birih da hixbullah zuka fitar ya zama tamkar yankar wuka cewa ba za’a mika wuya ba, kuma ba za’a amince da tsagaita wuta na wucin gadi ba, kan duk wata yarjejeniya da take kasa da janyewar dukkan sojojin Isra’ila daga yankunan kasar ta labanon.