Iran Ta Musanta Kai Hare Hare Kan Kasar Saudia A Yakin Sa’o’i 16

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakaei ya bayyana cewa sojojin Iran basu kai wani hare kan kasar Saudia a yakin sa’o’ii 16 da

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakaei ya bayyana cewa sojojin Iran basu kai wani hare kan kasar Saudia a yakin sa’o’ii 16 da ta fafata da HKI ba.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto bakaei yana fadar haka a jawabi ga kafafen yada labarai da ya saba a ko wace ranar litinin a jiya, ya kuma kara da cewa sojojin JMI basa buye wuraren da take kai kaiwa hare hare a duk lokacinda bukatar hakan ta taso.

Yace sojojin Iran basu aki hari ba ba sa nufin kai hare a kan kasar Saudia a yakin sa’o’ii 16 da ta fafata da HKI ba.

Ya ce, mai yuwa HKI ko kuma wasu wadanda suke aiki tare da ita a yankin ne suke son haddasa rikici tsakanin kasashen yankin tare da wadannan ayyuka.

Ya kara da cewa a baya ma, HKI to wakilanta a yankin sun kai irin wadannan hare hare a lokacin yakin Gaza, saboda rikita al-amura a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted