hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta bukaci hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a hukumance ta ba da dama yan wasan kwallon iran su sanya bakin kyalle a lokacin karawarsu da kasar masar saboda yayi daidai da zagayowar ranar shahadar imam hussaini As,
wasan da aka tsara za’a buga ne a ranar 27 ga watan yuli, ya fado ne a daidai ranar Ashura wacce ake gudanar da zaman makoki na zagayowar shahadar imam hussaini As da iyalansa da sahabbnsa a karni na 7 bayan hijra. yace ana so yan wasan su sanya bakin kyalle domin nuna juyayi da girmamawa ga imam Hussain, kuma tana fatar hukumar fifa za ta bada damar yin hakan,
musulmi yan shi’a a fadin duniya ne ke gudanar da tarurrukan juyayin Ashura don nuna alhini da juyayi na abin da ya faru, bukatar ta iran tana zuwa ne a daidai lokacin da ake takaddama kan wani abu da ake kira abin alfahari ne da kasa mai masaukin baki take son kallo a lokacin wasan kasar Iran da kuma masar
dukka kasashen iran da masar sun yi watsi da bukatar ganin cewa ta yi hannun riga da koyarwar addinin da kuma aladunsu, kuma sun sha alwashin hadin guiwa wajen tunkarar lamarin.