Afirka Ta Kudu Ta Aike Da Tawagar Bincken Musabbabin Mutuwar Jakadanta A Birnin Paris

A ranar Talatar da ta shude ne dai aka ga gawar jakadan kasar Afirka Ta Kudu a kasar Faransa Nathi Matherhwa, da aka nuna cewa ya fado daga kan benen Hotel hawa na 22. Babban sufeton ‘yan sanan kasar ta Afirka Ta Kudu Fenni Masemola ya sanar da aikewa da tawagar masu bincike su biyar […]
Iran: Kungiyar Kwallon Raga Ta Mata Ta Ci Kofin Asiya

A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan. An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a […]
HKI Ta Kwace Kudin Gwamnatin Faladinu Dala Miliyan 7.5 Ta Rabawa Wasu Iyalan Yahudawa 41

Jaridar Ma’ariv ta HKI ta buga labarin da yake cewa gwamantin HKI ta kwace kudaden gwamnatin kwarya-kwarya ta Faladinu da sun kai dala miliyan 7.54 ta rabawa wasu iyalan yahudawa 41 da su ka riya cewa hare-haren Faladinawa sun yi sadaniyyar kashe musu ‘ya’ya da dangi. Jaridar ta kuma kara da cewa; An rabawa iyalan […]
Sojojin Sudan Sun Zargi Rundunar “RSF” Da Kai Hari Akan Cibiyoyin Fararen Hula

A yau Lahadi sojojin na kasar Sudan su ka sanar da cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta kai hari akan cibiyoyin fararen hula a birinin al-Abyadh, wanda shi ne babbar cibiyar gundumar Jahar Kurdufan Ta Arewa. Bayanin na sojojin kasar ya kara da cewa; rundunar ta RSF ya kai hari da jiragen sama […]
Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga- zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinu A London

Bayanan dake fitowa daga birnin London sun nuna cewa jami’an yan sanda sun kama akalla mutane 500 a daidai lokacin da ake gudanar da gagarumar zanga zanga nuna goyon bayan falasdinu da kuma yin tir da kisan kare dangi da HKI ke yi, Zanga-zangar ta fara ne daga wani dandali dake birnin London inda masu […]
Dakarun Sojin kasar Yamen Sun Harba Makamai Masu Linzami A HKI

Rahotanni sun bayyana cewa karan sautin gargadi ya cika ko ina a Isra’ila a daidai lokacin da dakarun sojin kasar Yaman suke harba makami mai linzami na Ballistic a Isra’ila. a ci gaba da mayar da martani da kasar yamen din take yi kan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a Gaza. An ji […]
Masar Ta Zargi Habasha Da karya Dokokin Kasa Da Kasa Kan Rikicin Madatsar Ruwan Kogin Nilu

Kasar Masar ta zargi Habasha da nuna halin ko in kula da irin illar da rashin baiwa madatsar ruwan kogin Nilu kulawa ta musamman ke haifarwa ga tsaro da lafiyar al’ummarta. Bala’in ambaliyar ruwan da ake fuskana a Sudan nada alaka da sakin ruwa da Habasha tayi, lamarin da zai jefa Masar cikin fargabar fuskantar […]
Shugaban Hamas Ya Bayyana A Fili Tun Bayan Harin Isra’ila A Kasar Qatar

Khalil Al-hayya babban jagoran kungiyar Hamas ya bayyana akaron farko tun bayan hari da HKI takai musu a birnin doha na kasar Qatar a kokarin ta ta yin a kashe dukkan shuwagabannin Hamas dake wajen. Jagororin gwagwarmaya ta hamas da suka jagorancin tawagar tattaunawa sun yi bayyani ga alum palasdinu game da kisan gillan da […]
Dubban Mutane Ne Suka Yi Zanga -Zanga Nuna Adawa Da Isra’ila A Athens.

Rahotanni sun bayyana cewa dubun dubatan mutane ne suka yi gagarumar zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Isra’ila a birnin Athens na kasar girka inda suka yi Allah wadai da Isra’ila kan kama masu rajin kare hakkin dana dam da Isra’ila ta yi, na tawagar bada agaji ta Sumud Flotilla da ta isa Gaza, kuma sun […]
The Guardian: Isra’ila ta azabtar da Greta Thunberg ‘yar kasar Sweden mai fafutuka

Jaridar The Guardian ta Burtaniya ta tabbatar da cewa ofishin jakadancin Sweden da ke Isra’ila ya sanar da ma’aikatar harkokin wajen kasar a Stockholm cewa Greta Thunberg ta fuskanci munanan yanayi a lokacin da take tsare. Jaridar ta bayyana cewa an ajiye Thunberg a cikin wani daki mai kazanta, inda ta yi fama da kurji […]
Iran ta bukaci a haramtawa Isra’ila shiga harkokin wasanni na duniya

Iran ta yi kira ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ta dauki matakin haramtawa Isra’ila shiga harkokin wasanni na kasa da kasa. A cikin wata wasika da ya aike zuwa ga ministocin harkokin wasanni na kasashe 57 na kungiyar ta OIC, ministan wasanni da matasa na kasar Iran Ahmad Donyamali ya bukaci […]
Sheikh Qassem: Falasdinawa ne suke da hakkin yanke shawara kan makomar Gaza

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa Palasdinawa ne kawai suke da hakkin shawara kan makomar yankin zirin Gaza, da kuma abin da suke ganin ya dace da hakan, yana mai jaddada cewa mika wuya ba dabi’ar Falastinawa ba ce. Dangane da shirin shugaban Amurka Donald Trump kan zirin Gaza, Sheikh […]
An yi gagarimar zanga zangar goyan bayan Falasdinu a Barcelona, Rome, da Paris

A turai ana ci gaba da zanga zangar neman kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza. Dubban daruruwan mutane ne suka gudanar da irin wannan zanga-zanga a birnin Rome jiya Asabar domin neman kawo karshen yakin Gaza tare da bayyana goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu. Zanga zangar a […]
Malawi : Mutharika ya yi rantsuwar kama aiki

A Malawi an rantsar da Peter Mutharika a matsayin shugaban kasar a karo na biyu. Mutharika, wanda ya taba zama shugaban kasar daga shekarar 2014 zuwa 2020, ya sake komawa kan kujerar shugabancin kasar bayan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 16 ga Satumba da ya gabata. Mutharika […]
Hamas: Ci gaba da kai hari kan Gaza ya fallasa karyar Netanyahu

Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta ce; ci gaba da kai munanan hare-hare da kisan kiyashi da Isra’ila ke yi kan al’ummar Palasdinu a Gaza ya fallasa ikirarin karya na Firayim Minista Benjamin Netanyahu kan rage ayyukan soji kan fararen hula. A cewar sanarwar, sojojin mamaya na Isra’ila (IOF) na ci gaba da aikata munanan […]