Afirka Ta Kudu Ta Aike Da Tawagar Bincken Musabbabin Mutuwar  Jakadanta A Birnin Paris

A ranar Talatar da ta shude ne dai aka ga gawar jakadan kasar Afirka Ta Kudu a kasar Faransa Nathi Matherhwa, da aka nuna cewa

A ranar Talatar da ta shude ne dai aka ga gawar jakadan kasar Afirka Ta Kudu a kasar Faransa Nathi Matherhwa, da aka nuna cewa ya fado daga kan benen Hotel hawa na 22.

Babban sufeton ‘yan sanan kasar ta Afirka Ta Kudu Fenni Masemola ya sanar da aikewa da tawagar masu bincike su biyar da za su hada karfi da takwarorinsu na Faransa domin gudanar da bincike akan musabbabin mutuwar jakadan.

A ranar Litinin din makon da ya shude ne dai matar jakadan ta sanar da cewa ya bace, lamarin da ya bude kofar bincike da ta kai ga ganin gawarsa a kasan Hotel din Hyatt Regency a ranar Talata.

Wani jami’in ‘yansanda Faransa ya fada wa manema labaru cewa; jakadan na Afirka Ta Kudu, ya aike wa da maidakinsa sako ta waya yana mai neman gafararta akan cewa zai kashe kansa.

Wasu rahotanni suna nuni da cewa a lokacin rayuwarsa a can kasar Afirka Ta Kudu, ya shiga cikin rikice-rikice masu yawa da su ka hada da hannu a kashe masu ma’aikatan hako ma’adanai 34 a lokacin da suke zanga-zanga a 2012.

Haka nan kuma an zarge shi da batutuwa masu alaka da cin hanci da rashawa, saboda kusancinsa da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments