Sojojin Sudan Sun Zargi Rundunar “RSF” Da Kai Hari Akan Cibiyoyin Fararen Hula

A yau Lahadi sojojin na kasar Sudan su ka sanar da cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta kai hari akan cibiyoyin fararen hula

A yau Lahadi sojojin na kasar Sudan su ka sanar da cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta kai hari akan cibiyoyin fararen hula a birinin al-Abyadh, wanda shi ne babbar cibiyar gundumar Jahar Kurdufan Ta Arewa.

Bayanin na sojojin kasar ya kara da cewa; rundunar ta RSF ya kai hari da jiragen sama marasa matuki na kunar bakin wake, akan wasu sansanoni na farar hula da su ka hada Asibiti da makarantu, da hakan keta dokokin kasa da kasa ne.

Sojojin sun kuma ce, wadannan hare-haren sun kuma yi barna akan gidajen fararen hula a cikin unguwannin gari, sai dai babu rahoto akan asarar rayuka.

Sojojin na Sudan sun kuma bayyana cewa Abinda ya faru ba nasara ba ne ga rundunar kai daukin gaggawar, asara ce ta fuskar kyawawan halaye domin cutar da ‘yan kasa ne da ba su ji ba su gani ba.

 A cikin watan Febrairu ne dai sojojin na Sudan su ka sanar da yin nasarar kawo karshen killace garin Abyadh da rundunar kai daukin gaggawar ta yi.

Garin na Abyadh yana cikin manyar biranen kasar ta Sudan, kuma anan ce babar shalkwatar rundunar ta 5 ta sojan kasa take.

Tun a tsakiyar watan Aprilu na 2023 ne dai yaki ya barke a tsakanin rundunar kai daukin gaggawa da sojojin Sudan wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan da sun kai 130,000 kamar yadda MDD ta bayyana. Da akwai wani adadin mutanen kasar da sun kai miliyan 15 da su ka yi hijira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments