Shugaban Hamas Ya Bayyana A Fili Tun Bayan Harin Isra’ila A Kasar Qatar

Khalil Al-hayya babban jagoran kungiyar Hamas ya bayyana akaron farko tun bayan hari da HKI takai musu a birnin doha na kasar Qatar a kokarin

Khalil Al-hayya babban jagoran kungiyar Hamas ya bayyana akaron farko tun bayan hari da HKI takai musu a birnin doha na kasar Qatar a kokarin ta ta yin a kashe dukkan shuwagabannin Hamas dake wajen.

Jagororin gwagwarmaya ta hamas da suka jagorancin tawagar tattaunawa sun yi bayyani ga alum palasdinu game da kisan gillan da HKI ta yi da ya ci rayukan mutane 6, cikin har da dan shugaban kungiyar maai suna Hammam, da shugaban ofishinsa jihad labad, da dai sauran mutanen da abin ya  ritsa da su.

Shugaban yace ba zai iya banbancewa tsakanin mutanen da aka ritsa da su ba da sauran mutane gaza, wanda ake kashewa a kowacce rana, sakamakon mummunar Taddanci da gwamnatin yahudawa sahyuniya ke yi , na kisan kare dangi da ta fara tun daga watan oktoban shekara ta 2023.

Daga karshe ya hayya ya jinjinawa yan gwagwarmayar falasdinu dake tsayin daka fiye da qarni na fuskanta isra’ila, da sauran tsare tsaren kasashen yamma da zimmar karfafa mata guiwa na ganin hakarta ta cimma ruwa ta hanyar ci gaba da kashe alumma falasdinu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments