Jaridar Ma’ariv ta HKI ta buga labarin da yake cewa gwamantin HKI ta kwace kudaden gwamnatin kwarya-kwarya ta Faladinu da sun kai dala miliyan 7.54 ta rabawa wasu iyalan yahudawa 41 da su ka riya cewa hare-haren Faladinawa sun yi sadaniyyar kashe musu ‘ya’ya da dangi.
Jaridar ta kuma kara da cewa; An rabawa iyalan yahudawan kudin da sun kai Shakel miliyan 25 wanda shi ne kwatankwacin Dala miliyan 7.54, ta hannun lauyoyinsu.
Haka nan kuma jaridar ta ce hukumar dake kula da haraji da ke karkahsin ma’aikatar shari’a ce ta aiwatar da raba kudin a matsayin abinda su ka kira diyyar ayyukan t’addanci.!
Jaridar ta kuma ce tun a 2019 ne wadannan ‘yan sahayonioyar su ka bukaci a biya su kudaden.
HKI ta debi wadannan kudadan ne da daga kudaden hukumar Falasdinu da take rike da su da sun kai Dala miliyan 20 da 400,000.
Dukkanin kudaden da hukumar Falasdinawa a karkashin Mahmud Abbas Abu Mazin take amfani da su, suna biyowa ne ta Bankunan HKI, sai kuma ta cire haraji sannan ta mika musu.