Malawi  : Mutharika ya yi rantsuwar kama aiki

A Malawi an rantsar da Peter Mutharika a matsayin shugaban kasar a karo na biyu. Mutharika, wanda ya taba zama shugaban kasar daga shekarar 2014

A Malawi an rantsar da Peter Mutharika a matsayin shugaban kasar a karo na biyu.

Mutharika, wanda ya taba zama shugaban kasar daga shekarar 2014 zuwa 2020, ya sake komawa kan kujerar shugabancin kasar bayan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 16 ga Satumba da ya gabata.

Mutharika wanda farfesan shari’a ne ya sami kuri’u miliyan 3 kwatankwacin kashi (56.8%) a kan abokin hamayarsa Lazarus Chakwera na kusan miliyan 1.8 (33%).

Peter Mutharika ya yi rantsuwar ne a matsayin shugaban kasar Malawi na bakwai a wani biki da aka shirya a filin wasa na Kamuzu.

A cikin jawabinsa na farko, Mutharika ya bayyana cewa “lokacin farin ciki ‘’ wawashe dukiyar gwamnati ya kare”.

Ya ce gwamnatinsa za ta himmatu wajen maido da gaskiya da inganci a aikin gwamnati, a kasar da ya ce ta duk ‘yan Malawi ce ba tare da la’akari ba da siyasa, al’adu, ko addini.

Bikin ya samu halartar shugabannin Afirka da dama da suka hada da shugaban kasar Mozambique Daniel Chapo da shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da firaministan Tanzaniya Kassim Majaliwa da ministocin kasashen Angola da Namibiya da Zambia da kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted