A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan.
An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a yau Lahadi da samun galabar Iran.
Tun da fari kungiyar kwallon ragar ta Iran ta sami nasarori har sau uku a jere, da a karshe ta kai ga samun nasara akan mai masaukin baki kasar Uzbakestan.
Mai bayar da horo ga ‘yan wasan Li Du Hi, ta bayyana jin dadinsa da nasarar da su ka samu, musamman saboda wannan ne karon farko aka sami wannan irin nasarar.