Dakarun Sojin kasar Yamen Sun Harba Makamai Masu Linzami A HKI

Rahotanni sun bayyana cewa karan sautin gargadi ya cika ko ina a Isra’ila a daidai lokacin da dakarun sojin kasar Yaman suke harba makami mai

Rahotanni sun bayyana cewa karan sautin gargadi ya cika ko ina a Isra’ila a daidai lokacin da dakarun sojin kasar Yaman suke harba makami mai linzami na Ballistic a Isra’ila. a ci gaba da mayar da martani da kasar yamen din take yi kan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a Gaza.

An ji karar fashewar wasu abubuwa a tsakiyar Isara’ila , ina da wasu ke bayyana cewa da dukkan alamu makaman masu linzami ne da kasar Yaman ta harba da ake kokarin kakkabe su,

Kafar labaran HKi ta tabbatar da cewa an rufe sararin samaniyar filin hawa da saukar jiragen sama na ben Gurion da aka rufe shi na wucin gadi saboda hare-haren da dakarun sojin kasar yaman ke kai wa, da haka ke nuna yanayin zaman dar-dar da ake ciki a HKI.

Hare-haren na makamai masu linzami sun haifar da tsoro tsakanin mazauna yanki inda ya tilastawa dubban yahudawa tserewa domin neman mafaka don tsira da rayukansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments