Dubban Mutane Ne Suka Yi Zanga -Zanga Nuna Adawa Da Isra’ila A Athens.

Rahotanni sun bayyana cewa dubun dubatan mutane ne suka yi gagarumar zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Isra’ila a birnin Athens na kasar girka inda suka

Rahotanni sun bayyana cewa dubun dubatan mutane ne suka yi gagarumar zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Isra’ila a birnin Athens na kasar girka inda suka yi Allah wadai da Isra’ila kan kama masu rajin kare hakkin dana dam da Isra’ila ta yi, na tawagar bada agaji ta Sumud Flotilla da ta isa Gaza, kuma sun yi ta rera taken yanci ga falasdinawa.

Wannan zanga zangar tana kara nuna yadda alamarin faladinu musamman halin da ake ciki a gaza ya yadu a fadin duniya, kuma ya nuna irin yadda mutane suke nuna goyon bayansu ga alummar falasdinu.

Sjoojin ruwan HKi sun kai hari kan tawagar Sumud Flotilla suka tsayar da jirgin ruwan suka cafke dukkan matukan jirgin , tawagar na kan hanyar isa zuwa yankin gaza ne domin karya killacewar da Isra’ila tayi wa yankin ,da kuma isar da kayan agaji ga alummar Gaza,

Yanzu haka dai direban jirgin ruwan da kan Girka ya fara yajin cin abinci a inda isra’ila ke tsare da shi,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments