Hamas: Ci gaba da kai hari kan Gaza ya fallasa karyar Netanyahu

Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta ce; ci gaba da kai munanan hare-hare da kisan kiyashi da Isra’ila ke yi kan al’ummar Palasdinu a Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta ce; ci gaba da kai munanan hare-hare da kisan kiyashi da Isra’ila ke yi kan al’ummar Palasdinu a Gaza ya fallasa ikirarin karya na Firayim Minista Benjamin Netanyahu kan rage ayyukan soji kan fararen hula.

A cewar sanarwar, sojojin mamaya na Isra’ila (IOF) na ci gaba da aikata munanan laifuka da kisan kiyashi a duk fadin zirin Gaza, inda a cikin kasa da sa’oi 24 Isra’ila ta kashe Falastinawa Fararen hula sama da 70, da suka hada da mata da kananan yara.

Kungiyar Hamas ta sake sabunta kiran da take yi ga kasashen duniya da na larabawa da na Musulmi  da su sauke nauyin da ya  rataya a wuyansu, inda ta bukaci daukar matakin gaggawa na kariya da taimaka ma  al’ummar Palastinu da kuma yin matsin lamba don kawo karshen kisan kiyashi da yunwa da ke ci gaba da lakume rayukan al’ummar Gaza.

Har ila yau, kungiyar ta yi kira ga ‘yantattun mutane a duniya da su ci gaba da kara kaimi ga fafutukarsu wajen nuna goyon goyon baya ga al’ummar Falastinu, da kuma kalubalantar zaluncin da suke fuskanta, da kuma daukar matakan ladabtarwa na shari’a a kan Isra’ila a mataki na kasa da kasa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Isra’ila ta amince da mataki na farko na janyewa daga wasu yankuna na Gaza, lamarin da ya ce na a matsayin wani bangare na tattaunawar da ake yi na tsagaita wuta a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments