An yi gagarimar zanga zangar goyan bayan Falasdinu a Barcelona, ​​​​Rome, da Paris

A turai ana ci gaba da zanga zangar neman kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza. Dubban daruruwan

A turai ana ci gaba da zanga zangar neman kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza.

Dubban daruruwan mutane ne suka gudanar da irin wannan zanga-zanga a birnin Rome jiya Asabar domin neman kawo karshen yakin Gaza tare da bayyana goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu.

Zanga zangar a turai na ci gaba da bazuwa ne bayan da Isra’ila a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kame jiragen ruwan ‘yan fafatuka dake dauke da kayan agaji zuwa ga al’ummar Gaza.

A cewar hukumomi mutane 250,000 ne suka halarci zanga zangar ta goyan bayan Falasdinu a birnin Rome.

A tsakiyar birnin Barcelona, ​​dubun dubatar mutane ne suka yi maci na goyan bayan falasdinu, tare da neman kawo karshen cinikin makamai da Isra’ila.

Bayanai sun ce masu zanga-zanga 70,000 ne suka yi tattaki cikin lumana a kan titunan tsakiyar birnin, suna rera taken “kaurace wa Isra’ila!” sannan yanci ga “Palastinu “

A Madrid, kusan mutane 92,000 ne suka yi tattakin goyan bayan Falasdinu, a cewar gwamnatin Madrid.

A birnin Landan, mutane dubu guda ne suka shiga zanga-zangar nuna goyon bayansu Falasdinu duk da kiraye-kirayen da gwamnati da ‘yan sanda suka yi na kada su gudanar da zanga-zangar saboda harin da aka kai kan wurin ibadar yahudawa a makon nan.

Bayanai sun ce an cafke mutane sama da 400 cikin wadanda suka shiga zanga zangar.

A Faransa, ma an yi zanga-zangar tare da nuna goyon baya ga ayyukan isar agaji zuwa Gaza tare da yin kira ga Emmanuel Macron da ya kakaba wa Isra’ila “takunkumi” don cilas ta mata janye shingen da ta yi wa yankin Falasdinun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted