Jaridar The Guardian ta Burtaniya ta tabbatar da cewa ofishin jakadancin Sweden da ke Isra’ila ya sanar da ma’aikatar harkokin wajen kasar a Stockholm cewa Greta Thunberg ta fuskanci munanan yanayi a lokacin da take tsare.
Jaridar ta bayyana cewa an ajiye Thunberg a cikin wani daki mai kazanta, inda ta yi fama da kurji da bushewar fata, kuma an hana ta isasshen ruwa da abinci.
Jaridar ta ruwaito wata mai fafutuka ta Sweden tana cewa ta ga “masu tambayoyi suna tilasta mata (Thunberg) ta daga tutar Isra’ila.”
Wani mai fafutuka ya kuma ce, “Sun ja gashin Greta, suka yi mata duka, kuma suka tilasta mata sumbatar tutar Isra’ila,” ya kara da cewa sun yi duk abin da za su yi na cin zarafi a kanta a matsayin gargadi ga wasu.
Wani mai fafutuka ya ba da rahoton cewa “sun nannade Greta a cikin tutar Isra’ila tare da nuna ta kamar kofin gasa.”
Dakarun mamaya na Isra’ila sun kama ‘yar gwagwarmayar Sweden Greta Thunberg da wasu masu fafutuka daga kasashe daban-daban a lokacin da suke cikin jirgin “Global Resilience Flotilla”, wanda ya tashi don karya shinge da killacewar da aka yi wa Gaza, bayan harin da Isra’ila ta kai wa jiragen Ruwan da suke dauke da su.