Kasar Masar ta zargi Habasha da nuna halin ko in kula da irin illar da rashin baiwa madatsar ruwan kogin Nilu kulawa ta musamman ke haifarwa ga tsaro da lafiyar al’ummarta.
Bala’in ambaliyar ruwan da ake fuskana a Sudan nada alaka da sakin ruwa da Habasha tayi, lamarin da zai jefa Masar cikin fargabar fuskantar matsalolin da zasu shafi lafiya da dukiyoyin ‘yan kasar.
A watan da ya gabata ne Habasha ta kaddamar da katafariyar madatsar ruwan mafi girma a nahiyar Afrika wadda ta faro aikin gininta tun a shekarar 2011, aikin da ya haddasa rikici tsakanin kasar da makwabciyarta Masar.
Habasha kasa ta biyu mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika da mutane fiye da miliyan 120, ta kashe kuɗin da ya kai dala biliyan 5 wajen ginin wannan madatsar ruwa a saman kogin Nilu da ke sahun madatsun ruwa masu samar da lantarki guda 20 mafiya girma a duniya, da nufin habaka tattalin arziƙinta, duk da cewa wannan aiki ya haddasa gagarumin rikici tsakaninta da makwabtanta irin Masar da Sudan.