Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga- zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinu A London

Bayanan dake fitowa daga birnin London sun nuna cewa jami’an yan sanda sun kama akalla mutane 500 a daidai lokacin da ake gudanar da gagarumar

Bayanan dake fitowa daga birnin London sun nuna cewa jami’an yan sanda sun kama akalla mutane 500 a daidai lokacin da ake gudanar da gagarumar zanga zanga nuna goyon bayan falasdinu da kuma yin tir da kisan kare dangi da HKI ke yi,

Zanga-zangar ta fara ne daga wani dandali dake birnin London inda masu zanga-zangar suka yi kira ga gwamnatin birtaniya da ta cire suna yan ta’adda a lamarin falasdinawa.

Hukumar yan sanda ta birnin London ta ce kimanin mutane 492 ne aka kama wadanda ke da shekaru 18 zuwa 89 sai dai har yanzu guda 297 suna tsare yayin da aka yi bilin sauran,

Daga lokacin da Isra’ila ta fara kai hare-haren ta’addanci a yankin gaza daga ranar 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 akalla mutane fiye da dubi sittin ne suka rasa rayukansu yayin da 169430 kuma suka jikkata mafi yawancinsu mata ne da yara kanana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments