Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 15 A Wani Hari Kan Makarantar MDD

Rahotanni daga Falasdinu na cewa sojojin Isra’ila sun kai hari kan wata makarantar da MDD ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu (UNRWA) a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da jikkata wasu. Makarantar ta UNRWA, wacce ke dauke da daruruwan mutanen […]

Martanin Wasu Shugabannin Kasashen Duniya Kan Yunkurin Hallaka Trump

Shugabanni da gwamnatocin kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani game da yunkurin hallaka tsohon shugaban Amurka Donald Trump. Harbin da aka yi wa Trump, dan takarar shugabancin Amurka mai zuwa, a lokacin da yake gangamin yakin neman zabe ya fuskanci martani da dama musamman daga shugabannin kasashen duniya. Firayim Ministan Indiya Narendra […]

EU, Ta Yi Kakkausan Suka Kan Kazamin Harin Isra’ila A Gaza

Babban jami’in kula da harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell, ya yi kakkausar suka dangane da wani kazamin harin da Isra’ila ta kai zirin Gaza a baya-bayan nan wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 90 da suka hada da mata da yara tare da jikkata wasu fiye da 300, a yankin Al-Mawasi […]

Kasashen Sahel Na (AES) Sun Soki Shishigin AU A Harkokin Cikin Gidan Kasashen Su

Hukumomin mulkin soji na kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da suka hade a cikin sabuwar kungiyar hadin kan yankin Sahel (AES), sun yi tir da abinda suka kira shishigi na kungiyar Tarayyar Afirka a al’amuran cikin gidan kasashensu biyo bayan wani jami’in kungiyar ta AU, ya soki matakin ficewarsu daga ECOWAS. “Kwamishanan harkokin […]

Gwamnatin Sudan: Abin da ya faru a Geneva ya saba wa shawarwarin Jeddah

Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa, bisa la’akari da irin aikin da nauyin da take da shi na wajibcin kiyaye dokokin jin kai na kasa da kasa, da kuma kishinta na hadin gwiwa da kyakkyawar alaka da MDD, ta amince da shiga Tattaunawar a birnin Geneva na kasar Switzerland game da halin da ake ciki […]

NANS: Cire Tallafin Mai A Najeriya Bai Haifar Da Da Mai Ido Ba

Kungiyar Daliban Najeriya (NANS), ta shaida wa Shugaba Bola Tinubu cewa matsalar man fetur na ƙara ta’azzara a Najeriya, kuma cire tallafin bai haifar da ci gaban da ake tsammani ba. NANS, ta ce cire tallafin ya jawo matsaloli masu yawa ga ’yan Najeriya kuma ya haifar da ƙarancin man fetur maimakon wadatarsa. Sun bayyana […]

Sanata Bernie Sanders ya yi kira ga Amurkawa kada su kawar da kai daga yakin Gaza

Sanata Bernie Sanders ya yi kira ga al’ummar Amurka da kada su bari guguwar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar ta kawar da hankulansu daga babban bala’in da ke faruwa a Gaza. “A yayin da yawancin kafofin watsa labarai suka mayar da hankali kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar Amurka, dole ne mu ci gaba da […]

Kasar Iran Ta Yi Tsokaci Kan Ayyukan Ta’addancin Yahudawan Sahayoniyya ‘Yan Mamaya

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tsokaci game da laifukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a garin Khan Yunus na Falasdinu Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani da yake tsokaci kan kisan gillar birnin Khum Yunus, ya jaddada cewa: Kai hare-haren wuce gona da iri kan tantunan ‘yan gudun hijira a yankunan […]

An Yi Yunkurin Kashe Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump A Lokacin Yakin Neman Zabe

An yi yunkurin halaka tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hanyar harbinsa da bindiga a yayin yakin neman zabe Rahotonni sun bayyana cewa: Lamarin harbin tsohon shugaban na Amurka Donald Trump ya haifar da firgici a fagen siyasar Amurka, musamman ganin yadda ya bar fagen yakin neman zaben cikin jini. Kafofin yada labaran Amurka […]

Sayyid Nasrullahi Ya Ce Mujahidai Zasu Murnar Samun Nasara A Kan Yahudawan Sahayoniyya

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ya jaddada cewa: Za a kawo karshen yakin Ambaliyar Al-Aqsayayin da dukkan ‘yan gwagwarmaya suke cikin murnar samun nasara Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyed Hassan Nasrallah ya bayyana a yammacin jiya Asabar cewa: Dukkan ‘yan gwagwarmaya za su kasance cikin murna yayin kawo karshen yakin Ambaliyar Al-Aqsa suna […]