Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ya jaddada cewa: Za a kawo karshen yakin Ambaliyar Al-Aqsayayin da dukkan ‘yan gwagwarmaya suke cikin murnar samun nasara
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyed Hassan Nasrallah ya bayyana a yammacin jiya Asabar cewa: Dukkan ‘yan gwagwarmaya za su kasance cikin murna yayin kawo karshen yakin Ambaliyar Al-Aqsa suna madaukaka wadanda suka yi nasara, domin wannan shi ne alkawarin Allah ga muminai da mujahidai.
A cikin jawabin da ya gabatar kai tsaye ga al’umma, Sayyid Nasrallah ya tabbatar da cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya sun yi wani gagarumin kisan kiyashi kan mutanen da suka rasa matsugunansu a garin Al-Mawasi da ke Khan Yunus, bayan haka kuma sun kafa hujjar cewa suna son kai wa shugabannin ‘yan gwagwarmaya hari ne… Shin akwai wani zalunci da wuce gona da iri da suka shige haka a doron kasa?
Haka nan Sayyid Nasrallah ya jaddada cewa: Kula da batun Falasdinu, alhaki ne a kanmu da tausaya a cikin zukatanmu da bukatar gudanar da addu’o’i da furta matsayin siyasa da kare hakkokin Falasdinawa a kafafen watsa labarai da kuma yin tofin Allah tsine kan musguna musu da ake yi.
Yana mai jaddada cewa: Babban matakin tallafa wa Falasdinawa shi ne karfafa su da kayan aiki, wato gabatar musu da kudi, kuma duk wanda yake da damar gabatar da tallafin kudi, to alhakin da ya rataya a wuyarsa ne ya tallafa wa Falasdinawa.