Isra’ila ta sake yin fatali da muhimman batutuwa da tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza ta kunsa

An dakatar da tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza har sai lokacin da Isra’ila ta nuna da gaske take yi  wajen cimma yarjejeniya, kamar yadda

An dakatar da tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza har sai lokacin da Isra’ila ta nuna da gaske take yi  wajen cimma yarjejeniya, kamar yadda wasu majiyoyi biyu na Masar suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A halin da ake ciki, wasu majiyoyin tsaron Masar sun tabbatar wa kafar yada labarai ta Al-Ikhbariya ta Masar cewa, an dakatar da tattaunawar tsagaita wuta bayan tattaunawar kwanaki uku da ta kasa cimma matsaya.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, Masar ta yi kira ga Isra’ila  da kada ta  kawo cikas ga tattaunawar tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ko kuma gabatar da wasu sabbin bukatu da suka saba wa abin da aka amince da su, a cewar Al-Ikhbariya.

“Isra’ila” tana kokarin kawar da ra’ayoyin jama’a, a cewar majiyar, ta hanyar “bata lokaci yayin tarurruka na yau da kullun don nisantar da ra’ayin jama’ar Isra’ila daga cimma matsaya, don kaucewa rugujewar kawancen gwamnatin yaki da Neyanhu ke jagoranta.”

A baya wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa Masar ta nanata ficewar Isra’ila gabaki daya daga mashigar Rafah daga bangaren Falasdinawa.

Majiyar ta yi nuni a cikin wata sanarwa da ta aikewa Al-Ikhbariya cewa, Masar ta jaddada wajabcin bude dukkan mashigai  na kasar tare da zirin Gaza nan take, tare da jaddada matsayinta dangane da wajibcin Isra’ila ta ba da damar ‘yancin zirga-zirgar da ake yi a wadannan wurare domin ayyukan jin kai, da kuma ayyukan likitoci masu bayar da agajin gaggawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments